Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) - ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Birnin Karbala Mai Tsarki, da yammacin yau Alhamis, ya shaida gagarumin taron jana'izar girmamawa ga gawarwakin wasu shahidai da suka yi shahada sakamakon hare-haren Amurka da Saudiya masu yaudara.
An fara taron jana'izar ne tare da halartar jami'ai da ɗimbin jama'a, inda mahalarta suka yi Allah wadai da maimaita hare-haren rashin kunya kan dakarun Hashdush-Sha'abi (Dakarun Al’umma) waɗanda ke gudanar da aikin kiyaye tsaro da kwanciyar hankali kafatain kasar Iraqi.
Ra'ayinka